Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya Zasu Iya Shawo Kan Kalubalen Kayan Agaji

Yara 'yan gudun hijira da basu da iyaye

Jami’ai a Nigeria da na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice sun ce zasu iya shawo kan kalubalolin kayan agaji da mutanen yankin arewa maso gabashi kasar suke huskanta tun kafin abubuwa su dada lalacewa idan aka hanzarta sauraren bukatarsu na neman taimakon kayan agaji.

A kokarin da take yi na neman kudaden samarda kayan agaji a shekarar 2017 na asusun da aka kaddamar a ranar biyar ga watan Disamba din nan, MDD ta bukaci sama da dala biliyan daya don cimma bukatun mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita a yankin arewa maso gabashin Nigeria, wadanda kuma yawansu ya kai miliyan bakwai.

Wannan adadin kudin da ake bukata ya ninka abun da aka nema a shekarar nan ta 2016.

Zainab Ahmed, karamar minista a ma’aikatar shirye shirye da tsara kasafin kudin kasa, tace ana bukatar makudan kudaden ne saboda nasarar da sojoji suke samu a kokarinsu na sake kwato yankunan da a can baya suna hannun yan ta’addan Boko Haram.

Aikin agajin zai fi mayar da hankali ne a kan jihohi uku da wannan rikici yafi addaba da suka hada da jihohin Borno, Adamawa da Yobe. MDD ta fara tsara aikin agajin bisa la’akari da girman aikin da kuma wahala da mutanen ke sha.

Sama da mutane dubu 20 aka kashe kuma miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu a cikin Nigeria da makwabtanta tun shekarar 2009 da kungiyar Boko Haram ta soma kai hare-haren ta’addancinta a arewa maso gabashin kasar.