A Najeriya dai kusan kananan hukumomi 16 ne na jihohi biyar ke cikin wannan batu kuma wadannan yankuna sun hada da yankin kananan hukumomin Mubi ta arewa da Mubi ta kudu, sai karamar hukumar Toungo, da Ganye da kuma kananan hukumomin Gashaka, Kurmi, Sardauna na jihar Taraba.
Mrs Tiyasa Agustine na cikin matan da suka hallarci wannan gangami daga Ganye, tace zasu cigaba har sai hakarsu ta cimma ruwa.
A sakonsa ga mahalarta taron shugaban wannan fafutukar Farfesa Martin Chia Ateh,wanda har ila yau yake wa majalisar dinkin duniya aiki a matsayin jami’in tuntuba ta fannin diflomasiya, cewa yayi ‘’Dole a cigaba da fadakar da al’umma,tunda ba tun yau ba kotun duniya ta bada hukunci kan lamarin kuma duk kasashen da abun ya shafa sun sani har yana cikin taswirar duniya.Wasu yan abubuwa kadan wato technicality ne suka rage,’’ da sannu za’a kai ga cimma ruwa.
Saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz
Your browser doesn’t support HTML5