A karkashin shugabancin Mr. Chambas na Majalisar Dinkin Duniya sansan biyu sun sake nazari kuma sun amince kan mahimmancin warware duk batutuwa ta wajen fidda taswira da zai bada fifiko inda aka fuskanci gardama cikin gaggawa.
Suna son kammala aikin shata iyakoki da kuma fara ayyukan more yaruwa ga mutanen da canjin kan iyakokin ya shafa domin karfafa masu gwuiwa da kuma samar da kudade ga asusun da aka bude na musamman domin kammala sauran ayyuka da suka rage.
Mr. Chambers yace ya yi maraba da irin halayen da shugabannin tawagogin kasashen biyu suka nuna. Ya kuma yaba masu saboda dukufar da suka yi na kammala shata kan iyakoki da kuma bada gudummawar gaggawa ga al'umma da aikin ya shafa.
A nasa bangaren shugaban tawagar Kamaru Ahmadu Ali ya bayyana anniyar gwamnatinsa na ganin an warware duk sauran batutuwan da suka rage saboda aiwatar da hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke.
Da yake magana ministan shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya sake nanata kudurin Najeriya na ganin an kammala shata iyaka akan yanki mai tsawon kilomita dari. Kuma zata dauki duka matakan tunkarar batutuwan da suka rage.
Najeriya da Kamaru zasu sake zama cikin watan Nuwamban bana.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5