Rahotan da kungiyar ta fitar na nuni da cewa Najeriyar tazo ta 146 a jerin kasashen da suka fi kowacce ‘kasa cin hanci a duniya.
Ga dukkan alamu an samu takaddama tsakanin kungiyar Transparency International da hukumomin dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, game da rahotan da ke cewa maimakon cin hanci ya ragu, karuwa yake a kasar.
A rahotan da aka fitar cikin kasashe 180, Najeriya ita ce ta zo ta 146 a shekarar 2019. Wanda haka ke nuna cewa Najeriya ta ci baya. Sai dai Najeriya na cewa wannan rahotan bai yi mata adalci ba.
Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya bayyanawa sashen Hausa irin kokarin da gwamnatinsu take yi a yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar samar da dokoki.
Biyo bayan sukar da Najeriya ta yi game da rahotan, Muryar Amurka ta tuntubi shugaban kungiyar a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani, wanda ya ce abu ne a bude karara domin duk mutumin da ke ciki ko wajen kasar ya san cewa akwai cin hanci da rashawa a kasar.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Farouk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5