Najeriya Ce Kasa Ta Goma Cikin Kasashen da Suka Daidaita Al’amuran Yanayin Kasuwanci

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da sauran shugabannin kasashen yammacin Afirka a taron habaka tattalin arzikin yankin

A nahiyar Afirka Najeriya na cikin kasashe 10 dake kan gaban samar da yanayin da ya dace na gudanar da kasuwanci a saukake yadda kasashen ketare ka iya saka jari su kuma fitar da ribarsu cikin ruwan sanyi

Wani bincike da Bankin Duniya ya wallafa ya nuna cewa Najeriya ce kasa ta 10 a jerin kasashen da suka samu kyautatuwar yanayin gudanar da hada hadar kasuwanci da saka jari a Afrika, sai dai kwararrun kan lamuran tattalin arziki sun ce akwai sauran aiki a gaban mahukuntan Najeriya din.

Baya ga Najeriya, rahotan binciken, wanda aka yi daga watan Yunin bara zuwa Yunin bana, ya ce kasashen Malawi da Zambia na cikin goman farko na kasashen da aka gudanar da binciken.

Dr Lawan Habib Yayhaya dake zaman kwararre kan al’amuran tattalin arziki da hada hadar kudade, ya fayyace batutuwan da hukumomin tattalin arziki na duniya ke la’akari da su wajen ayyana kyautatuwar hanyoyin kasuwanci da zuba jari a kasa. Wadanan ko sun hada da kasa ta zama kan turbar Dimokradiya, tana da tsaro da kuma, uwa uba, bankunan masu karfi.

Alhaji Ahmad Madaki dake zaman Daraktan shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na Hukumar Kula Da Harkokin Kanana Da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya yace hatta a matakin kananan ‘yan kasuwa na cikin gida an samu wannan kyautatuwar yanayin gudanar da kasuwanci.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ce Kasa Ta 10 Cikin Kasashen da Suka Daidaita Alamuran Yanayin Kasuwanci - 3' 52"