Najeriya Ce Kan Gaba Wajen Yada Polio A Duniya

Ana ma jaririya rigakafi a Kano, Najeriya

Kungiyar Likitocin Harhada Magunguna ta Najeriya ta ce rashin sanya 'ya'yanta cikin wannan aiki, yana rage masa kaifi da baza kwayar cutar
Kungiyar Likitocin Harhada Magunguna ta Najeriya (Pharmaceutical Society of Nigeria) ta ce Najeriya ita ce kan gaba a yanzu wajen yadawa sauran kasashen duniya kwayar cutar nan da Polio ko shan inna.

Shugaban kungiyar, Olumide Akintayo, ya fada cewa a wasu kasashen duniyar kamar Amurka, ana gudanar da kashi 80 cikin 100 na ayyukan yin rigakafi ne a kantuna ko wuraren sayar da magunguna dake unguwanni ko gundumomi. Yace kwararrun likitocin magunguna, sune jama'a suke fara tuntuba idan su na da wata matsalar rashin lafiya.

Mr. Akintayo yace "Kashi 40 cikin 100 na dukkan yaran dake mutuwa su na kanana, ko matan dake mutuwa lokacin haihuwa a duk fadin duniya, ana samunsu ne a kasashe biyu tak a duniyar, a Najeriya da kuma Indiya. Menene dalilin haka? Saboda gwamnati a kasashen biyu tana yin ko oho da kwararrun likitocin harhada magunguna da wasu ma'aikatan lafiyar dake da kwarewar da zata iya taimakawa wajen rage wadannan mace-mace."

Yace a yanzu, "nan da mako uku zaka ji labarin cewa an samu sabbin yara guda uku da suka kamu da kwayar cutar Polio a nan Najeriya."