Najeriya: Ce-Ce Ku-Ce Kan Mayar Da Wa'adin Mulki Shekara 6

Majalisar Dokokin Najeriya

Ga dukkan alamu, takaddama ta kunno kai, bayan watsi da kudurin nan da aka nema domin baiwa Shugaban kasa da 'yan Majalisu damar yin wa'adin mulki daya na tsawon shekara 6 a Majalisar Dokokin Najeriya.

Kawunan 'yan Majalisar Dokokin sun rarrabu akan wannan batu yayin da wasu ke tunanin rudani zai kawo a harkar siyasar kasar, wasu na tunanin a kara yawan shekarun ya fi.

Senator Yusuf Abubakar Yusuf

Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya ce yana ganin bin tsarin zabe irin na kasar Amurka zai ba da dama a yi zabe a tsanaki.

Kuma in da son samu ne, a yi wa'adin mulki na shekara 8 a jere babu sabuntawa, saboda a samu natsuwa sosai a yi wa kasa aiki kafin a yi wani zaben.

Amma ga dan majalisar wakilai Sada Soli Jibiya, ya fi son a ci gaba da yadda ake tafiya na shekara 4-4 maimakon kawo rudani a kasa.

Ya kara da cewa, kuma idan an fara gyara kundin tsarin mulki domin kara shekaru, rage wa ba zai haifar wa kasar albarka ba.

Sai dai, shi kuma dan Majalisar wakilai Balarabe Abdullahi Salame, ya ce, yin shekara 6 kuma wa'adi daya din nan ya fi, saboda yana ganin zai zaburad da shugabanni su gaggauta yi wa kasa aiki, tun da sun san cewa ba za su sake dawo wa karagar mulki ba.

Wannan batu idan za a tuna, na wa'adin mulki na shekara 6 babu sabuntawa ya taba shan kaye a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

A saurari rahoto cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Ce-Ce Ku-Ce Kan Mayar Da Wa'adin Mulki Shekara 6