Najeriya: Buhari Ya Shawarci 'Yan Siyasa Su Guji Cakuda Addini Da Siyasa

Shugaba Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari har ila yau, ya yi kira ga wadanda ba su samu nasara a zaben fidda gwani a jam'iyyunsu ba, da su fifita zaman lafiyar kasarsu sama da bukatunsu na kansu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da su guji yin amfani da addini da kabilancin wajen cimma burinsu na siyasa.

Buhari ya yi wannan kira ne, a lokacin wani taron hadin gwiwa da ya tattaro mabiya addinai daban-daban, wanda ya gudana a Abuja, babban birnin kasar.

Shugaba Buhari wana ke neman wa'adi na biyu, ya kuma yi kira ga wadanda ba su samu nasara a zaben fidda gwani a jam'iyyunsu ba, da su fifita zaman lafiyar kasarsu sama da bukatunsu na kansu.

Ya kuma ce akwai hanyoyi da dama da mutum zai bi domin bayyana korafinsa da suka hada da kwamitocin sulhu da jam’iyyu suka tanadar da kuma kotunan kasa.

Saurari tattaunawar da Mahmud Lalo ya yi da Muhammad Yusuf Kanam mai sharhi kan al'amuran siyasa:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Buhari Ya Shawarci 'Yan Siyasa Su Guji Cakuda Addini Da Siyasa - 4'02"