Najeriya: Ana Zargin Wasu Jami'an Tsaro Da Yin Fashi

A Najeriya ana zargin wasu mutane da ake tsammani jami’an tsaro ne da yi wa tawagar 'yan kasuwa fashi akan babbar hanyar da ta ratsa jihohin Bauchi da Yobe zuwa jihar Borno.

Rahotannin da Muryar Amurka ta samu na nuni da cewa, da misalin karfe uku na asuban yau Talata ne a wani kauye mai suna Daruri dake karamar hukumar Dambam a jihar Bauchi, 'yan sanda masu sunturi akan babbar hanyar da ta ratsa jihohin suka kafa shinge suna tsare motoci.

A cewar wani mazaunin garin Dambam, a hirarshi dashi ta wayar tarho jami’an tsaron sun tube kayansu, suka sauya da kayan gida, sannan suka rufe fuskokinsu domin badda kamanni.

Jami’in hulda da jama’a na karamar hukumar Dambam ya bayyana cewa, ya gani da idonsa lokacin da aka tsare motoci kafin daga baya al'ummar gari suka tunkari wadanda suka tare hanyoyin da suka fahimci a gane su, sai suka tsere.

Sai dai da aka tuntubi DPO na 'yan sanda na karamar hukumar Dambam Haruna Yerima ta wayar tarho ya ce ba shine zai yi bayani ba, sai dai a sami kakakin hukumar 'yan sanda a Bauchi.

Duk kokarin da Sashen Hausa ya yi na neman jin ta bakin n kakakin hukumar 'yan sanda ta Bauchi kafin hada wannan rahoton ya cimma tura.

A saurari rahoton Abdulwahab Mohammed cikin sauti, daga jihar Bauchi,Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Ana Zargin Wasu Jami'an Tsaro Da Yin Fashi