Najeriya: Ana Nuna Fargaba Kan Wani Salon Sayen Katin Zabe

A lokacin da wata mata take kada kuri'arta a zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Legas a 2017 a Najeriya

Yayin da ake haramar soma babban zabe a Najeriya, yanzu haka wata sabuwa ta kunno a jihar Taraba inda wasu ke bi suna saye da daukan hotunan katunan zabe a hannu masu kada kuri'a.

Wannan lamari ya sa kungiyoyi da ke rajin kare tsarin mulkin dimokradiyya, yin kira da a yi hattara.

Kamar yadda rahotanni ke nunawa, wasu 'yan barandan siyasa ke shiga unguwanni domin saya ko daukan hotunan katunan zabe jama'a.

Wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz ya ji ta bakin wasu shaidun gani da ido, wadanda suka nemi a sakaya sunayensu.

"Wani gungun 'yan siyasa yana bi gida-gida yana ba da dubu daya-daya, ana ba shi katunan zabe yana daukan hotansa, ba mu san wacce manufa ce suka da ita ba," a cewar wani shaida.

Yanzu haka ma tuni kungiyoyin makiyaya a jihar suka farga tare da daukan gabaren wayar da kan makiyaya a rugogi, kamar yadda kakakin kungiyar Miyetti Allah a jihar ya tabbatarwa da Muryar Amurka.

Ana ta bangaren hukumar zabe ta INEC, ta ce ko da yake kawo yanzu, ba wanda ya sanar da Ita a hukumance , amma tuni ta dauki matakin wayar da kan al'umma.

"Ya rage ga kai mai kada kuri'a kada ka ba wani katinka, kada ka sayar da 'yancinka, mu kuma ba mu aiki wani," ya yi wannan aiki ba a cewar Mr. Fabian Yame Vwamhi, jami'in wayar da kan masu zabe ya gargadi jama'a da suke sa ido.

Ya kuma yi kira ga jama'a da su yi hanzarin fadawa jami'an tsaro idan suka ga wadannan mutane.

Kawo yanzu duk kokarin ji daga hukumomin tsaro, dangane da wannan lamari ya citura, yayin da wata majiya ke cewa tuni wasu 'yan sa-kai suka yunkuro don bankado wadanda ke da hannu a wannan badakalar sayen katunan zaben.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Ana Nuna Fargaba Kan Wani Salon Sayen Katin Zabe- 3'09"