Kodayake farashin neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya ya fi na kowani zabe tsada a tarihin Najeriya, inda na jam'iyyar APC mai mulki ma ya kai har Naira miliyan 100, hakan bai hana tarin 'yan takarar shugabancin tururuwa domin sayen takardar takarar ba. Yanzu yawansu ya kai 24 a karkashin APC kawai.
Ko a yankin yarbawa na kudu maso yanmacin Najeriya yanzu haka akwai 'yan takara da suka hada da Matainakin Shugaban Najeriya, Farfeasa Yemi Osinbanjo da Senator Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amuson, sai kuma tsohon shugaban majalisar Wakilai Hon. Dimeji Bankole da kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, kodayake dai masu kula da harkokin siyasar yankin na ganin har yanzu Bola Tinubu ne kan kaba a tsakanin 'yan takaran, amma dai neman hadin kai tsakanin 'yan takarar abu ne da ake bukata inji tsohon shugaban Jamiyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Ondo, Bisi Akande, wanda ya jagoranci taron wanda kuma yace a karshen sa, an cimma matsaya na ganin yankin ya fito da wanda zai gaji shugaba Buhari a shekara ta 2023.
To ko yaya magoya bayan wadannan 'yan takara na yankin yarbawan ke ganin wannan taro? Babangida Mani, mai goyon bayan Tinubu, da Abubakar na Babanyawo, mai goyon bayan Fayemi Kayode, sun ce akwai bukatar marawa 'yan takaran da ya dace baya, yayin da kowannensu ke goyon bayan gwaninsa.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5