Hukumar da ke kayyade farashin man fetur ta Najeriya ta fitar da sanarwar sake rage farashin litar man daga naira 123.50 zuwa 121.50, abin da masana a fannin tattalin arziki da ‘yan kasar suka ce ba a gani a kasa ba, ganni karo na uku kenan a cikin wannan shekarar ta 2020 ana rage farashin
Wannan sabon umarni na kunshe ne cikin sanarwar da aka aika zuwa ga ‘yan kasuwar man fetur a kasar.
Idan ba a manta ba a ranar 7 ga watan Mayu kamfani man feit na NNPC ya fitar da sanarwar rage farashin rubin adana man daga naira 113.28 zuwa 108 a duk fannin kasar.
Sai dai Alhaji Kasim kurfi masani kuma mai sharhi kan tattalin arziki kasa a Najeriya, ya ce wannan farashi ba ya tasiri ga 'yan kasuwa bare talaka da ke neman abin da zai kai bakin salati.
Biyo bayan wannan sanarwa ta rage tsohon farashin rubun adana man, an yi tsammanin sabon farashin da humakar da ke kayyade farashin man ta Najeriya za ta fitar ga ‘yan kasar, da ke ta sa ido mussamman a wannan yanayi da annobar cutar COVID-19 ta zai kawo sauki.
Wanna shi ne karo na uku da aka sauya farashin mai a Najeriya a cikin wannan shekarar ta 2020.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.
Your browser doesn’t support HTML5