Najeriya: Abubuwan Da Kasafin Kudin 2019 Ya Kunsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A kasafin na badi, kananan ayyuka za su lakume naira biliyan 4.4, manyan ayyuka za su ci naira biliyan 2.1.

Shugaba Mohammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin badi a gaban hadaddiyar Majalisar Dokokin Najeriya, wanda ya kama Naira Triliyan 8.8.

Gabatar da wannan kasafin kudin na zuwa ne watanni shida kacal da fara aiwatar da kasafin baan na 2018.

Shugaba Mohammadu Buhari dai ya kwashi sama da sa'a daya yana gabatar da kasafin kudin cikin ife-ife na ‘yan adawa a tsakanin ihun “Sai Baba Buhari” na masu goyon bayansa.

Wannan wata alama ce da ta nuna nuna rarrabuwar kawuna a bangaren manyan jam’iyyun kasar biyu da ke nuna za a ja daga a gabanin zabe mai zuwa.

A kasafin na badi, kananan ayyuka za su lakume naira biliyan 4.4, manyan ayyuka za su ci naira biliyan 2.1.

Ma'aikatar cikin gida ita ce ta samu kaso mafi tsoka da naira biliyan 569, sai ma'aikatar ilimi da naira biliyan 462, sai ma'aikatar tsaro mai naira biliyan 435.

Ita kuwa ma'aikatar kiwon lafiya ta samu naira biliyan 315.6.

Saurari rahoton Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Abubuwan Da Kasafin Kudin 2019 Ya Kunsa- 3'38"