Najeriya A Shirye Take Ta Lashe Kofin Zakarun Afrika

Tawagar Yan Wassan Kwallon Kafar Najeriya

A shirye shiryinta don ganin ta fafata a wasanta da kasar Seychelles, cikin wasan karshe na shiga gasar cin kofin nahiyar kasashen Afirka wanda za'ayi a kasar Masar a shekarar 2019.

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles dake tarayya Najeriya, ta fara karbar horo a filin wasa na tunawa da Stephen Keshi dake Asaba.

A ranar Talata da ta gabata ne Kocin kungiyar Gernot Rohr ya fara bada horo wa 'yan wasan Najeriya a Asaba, da misalin karfe hudu da rabi na yammaci agogon Najeriya.

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Najeriya NFF ta bada tabbacin isar wasu 'yan wasa filin horon wanda suka hada da Ahmed Musa, Paul Onuachu, Effiong Ndifreke, Leon Balogun, Troost-Ekong, Kenneth Omeruo, da Abdullahi Shehu.

Sauran 'yan wasan da suka samu isa Najeriya daga kasashen da suke wasa sune Wilfred Ndidi, Chidozie Awaziem, Moses Simon da kuna Jamilu Collins.

Sai dai hukumar tace tana sa ran isowar wasu 'yan wasa da suka hada Maitsaron raga Francis Uzoho, dan wasan tsakiya John Ogu da Oghenekaro Etebo, sai kuma 'yan wasan gaba kamar su Henry Onyekuru da Victor Osimhen.

Hukumar tace a ranar Laraba atisayen zai cigaba inda magoya bayan kungiyar da 'yan jaridu zasu samu halartar filin horon, don shaida wa da idanunsu da kuma ba wa 'yan wasan karfin gwiwa.

Tawagar Super Eagles wadda ta lashe kofin nahiyar ta Afrika sau uku,
zata kara da kasar Seyschelles ne a ranar Jumma'a 22 ga watan Maris na bana a filin wasa na Stephen Keshi dake Asaba, da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da Kasar Chadi.