NAIRA BILIYAN 10: Kudin Da Za a Kashe Kan Kidayar Al’ummar Najariya

Zabe a Jihar Bauchi

Tanadin da gwamnatin Najeriya ta yi na ware Naira biliyan 10 ya na ci gaba da haddasa mahawara a tsakanin al'ummar kasar a yayinda wasu ke kallon matakin a matsayin ci gaba wasu kuma na kallonshi a matsayia barnar kudi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a fitar wa Hukumar Kidayar Jama'a ta kasa Naira Biliyan 10 domin kirga yawan jama'a da ke kasar da ake sa ran farawa a shekara mai zuwa.

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja Mukaddashin Shugaban Hukumar Kidayar Jama'a Eyitayo Oyetunji yayi bayani cewa, tuni har an yi nasarar shata kananan hukumomi 228 a fadin jihohi 35 da birnin Taraiyya Abuja.

Masu goyon bayan wannan yunkurin sun bayyana cewa, kidayar jama'an kasa muhimmin ci gaba ne domin a samu alkaluma a matsayin ginshikin samar da ingantaccen shirin bunkasa da kuma raba albarkatun kasa da kuma samun daidaito a guraban ayyukan gwamnati da zai bada damar damawa da kowanne bangaren kasar. Suna masu fadin cewa babu yadda kasa za ta iya ci gaba ko kuma samar da kyakkyawan tsarin da zai biya bukatun al’umma ba tare da sanin yawansu ba.

wa-ya-karkatar-da-naira-2-67b-na-ciyar-da-yan-makaranta

hukumar-zaben-najeriya-ta-gaiyaci-kamfanoni-don-kera-ma-ta-naa-urar-kada-kuuri-a

manoman-najeriya-suna-fama-da-tsadar-abinci

To sai dai wadanda suke kushewa wannan yunkurin suna masu ra’ayin cewa, kashe wannan kudin a daidai wannan lokacin domin kidayar jama’a bai dace ba ganin yadda galibin al’ummar kasar ke zaune cikin matsanancin talauci da tsadar rayuwa. Sun yi misali da matsaloli da suka addabi kasar da suka hada da matsalar tsaro, da rashin ababan more rayuwa kamar ruwan sha da wutar lantarki da asibitai da hanyoyi da tabarbarewar harkokin ilimi da ya sa a halin da ake ciki kungiyar malaman jami’oi su ke yajin aiki.

Kasuwa a birnin Ikko

A maimakon kashe wannan makudan kudin kan kidayar al’umma, masu kula da lamura suka bada shawarar amfani da kudin wajen shawo kan matsalolin da suka zayyana da zai taimaka wajen gina kasa.

Bayanai na nuni da cewsa an gudar da aikin kidayar al’umma har sau biyu ana sokewa, da ya hada da aikin kidayar da aka yi a shekarar 1973 da 1991. Najeriya ta yi kidayar karshe wace ake amfani da ita a shekara 2006.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

NAIRA BILIYAN 10: Kudin Da Za a Kashe Kan Kidayar Al’ummar Najariya-3:00"