Majalisar Dinkin Duniya ta ce nahiyar zata bukaci akalla malamai miliyan 15 domin koyar da dalibai a makarantun firamare da na sakandare zuwa 2030.
Nahiyar Afirka tayi nasarar daukar Karin dalibai cikin shekaru 10 da suka gabata, to sai dai kuma an dade ana sanya ayar tambaya akan ingancin illimi a nahiyar a dalilin rashin ingancin malaman da suke koyarwakaramcin malaman book a nahiyar wanda ke da nasaba da karancin malamai a makarantun Afirka da dama.
Kungiyar da ke bibiyar al’amuran illimi, kimmiya da al’adu na majalisar dinkin duniya UNESCO ta ce duk da ‘yan nasarorin da nahiyar ta cimma wajen daukan malamai aiki cikin shekaru 5 din da suka gabata, harkar illimi na tafiyar hawainiya kana kasashe da dama suna bukatar kara yawan malaman da suke koyarwa atrick Nkenggne, babban mai sharhi ne a kungiyar ta UNESCO.
Ya ce wasu tsirarun malamai ne suke kula da karatun miliyoyin dalibai a nahiyar Afirka.
Ya sheda cewa, “a duk sa’adda ya kasance ajujuwa sun kasance cewa dalibai 100 ne a ko wani aji sabanin 50 da ya kamata ko kuma malami daya ya koyar da dalibai 40zuwa 50 kamar yadda aka tsara, to lallai wannan na bayyana karanci. A yayin da ajujuwan suka karu cikin wannan yanayain kuma, matsalar tana dada ta’azara.
UNESCO ta ce kafin Afirka ta kai ga cimma manufofinta na bangaren illimi, sai ta sake daukar malamai akalla miliyan 15 a matakin firamari da sekandare zuwa 2030. Kungiyar ta kuma sheda cewa, kasashen Afirka ta Tsakiya, Chadi, Mali da Nijar ne suke bukatar mafi yawan malaman firamare inda ake samun karuwar dalibai da kaso %6 cikin a kowace shekara.
UNESCO ta bukaci gwamnatoci a Afirka su yi nazari akan yawan malaman da suke bukata na shekaru 10 masu zuwa nan gaba, sannan tayi nazari kan irin horo ko dabarar da zata kaiga cimma bukatun ta na yawan malaman da ta ke bukata sannan kuma ta tabbatar da ta samar da wadattacen kudaden da za ta biya malaman da kuma horon da zata basu domin su dada samun gogewa.