Nahiyar Afirka Na Fama da Cutar Dimuwa - Farfasa Lumumba

Shugabannin kasashen Afirka

Kasashen Afirka har yanzu tamkar bayin kasashen Turai da suka yi masu mulkin mallaka ne saboda basu da tasu akidar ko inda suka sa gaba

Samun 'yancin kai da wasu kasashen Afirka suke buga kirji sun samu suna ne kawai domin da zara wani abu ya samesu sai su nufi kasashen da suka yi masu mulkin mallaka.

Matasan Afirka, kamar shugabanninsu basu mutunta duk abun da ya fito daga Afirka sai dai na Turai kama daga wakokin da suke ji, mawakan da suka fi so, kai hatta ma da abincin da suke ci.

Da zara wani babban mutum ya soma jin rashin lafiya sai ya ruga London idan Birtaniya ce ta yiwa kasarsa mulkin mallaka ko kuma Paris idan Faransa ce ta mallakesu.

Yau an ce babu bauta a duniya amma matasan Afirka don karankansu suna kai kansu kasashen Turai domin aikin bauta da suka fi gwammacewa dashi maimakon su yi aiki a kasashensu domin shugabanninsu barayi sun wawure arzikin kasa sun kai Turai.

Ga shirin Dimokradiya A Yau na Sahabo Aliyu Imam

Your browser doesn’t support HTML5

Nahiyar Afirka Na Fama da Cutar Dimuwa - Farfasa Lumumba - 9' 44"