Nagartatun Tituna na Habaka Tattalin Arzikin Kasa

Tituna

Sanin kowa ne cewar, mafi’akasarin abubuwan zamani suna tafiya ne da lokaci, kana da wasu ire-iren dokoki. Alallhakika duk wani abu da bature ya samar da shi to za’aga cewar wannan abun yana da tsarin yadda yakamata a tafiyar da shi da kuma hanyoyi da sukafi can-canta a gudanar da wannan abun. A tabakin wata Injiniyar tituna me suna Hajiya Maryam Balla, wadda tayi muna karin haske akan yadda yakamata ace anyi da kuma dokoki da suka kamata abi a yayin kirkirar titi.

Ta fara da cewar akwai bukatar a samar da duk masana harkar tituna a yayainda ake shirin fara wani aiki na titi, don ta haka ne kawai za’a iya samar da ingantacen titi da yakamata ace yakai tsawon shekaru 100, amma a irin yanayi na kasar Najeriya, baza a iya samar da hakaba, sai dai tayi nuni da cewar idan aka bi duk dokoki da aka shardanta na samar da masu bincike da duba yanayin wuri, yanayin kasar wuri, da yanayin yanki, wanda ana la’akari da wannan shima kamin a kaiga matsayar wane irin aiki ne za’a gudanar.

Ta kara da cewar ta samar da wadannan ka’idojin ne kawai za’a iya samun tituna masu yalwa da inganci. Kuma idan aka bi wadannan ka’idojin to lallai bashakka wannan wata hanyace da za’a kara karfin tattalin arzikin kasa da sama ma matasa aikin yi don ci gaban kasa baki daya. Babban kiranta a nan shine, yakamata mahukunta su bada kaimi wajen bin wadannan dokokin koda kuwa za’a kashe kudade masu yawane, amma idan aka duba alfanu da kuma taikaitama al’uma wahala, to za’aga cewar yin hakan ba asara bane.