NAFDAC Ta Ce A Guji Yin Amfani Da Wadannan Magungunan Tari

Magungunan tari da NAFDAC ta ce a guji yin amfani da su (Facebook/NAFDAC)

"Idan kun taba amfani da wadannan magunguna, kuma sun haifar muku da wata matsala, ku yi maza ku garzaya asibiti." In ji NAFDAC.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC a Najeriya, ta yi kira ga al’umar kasar da ta guji yin amfani da wasu magungunan tari da ke kasuwa.

NAFDAC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin.

“NAFDAC na sanar da jama’a cewa, akwai wasu magunguna biyu da ba su da inganci (gurbatattu) wadanda suka hada da Ambronol da DOK-1Max da aka gano a kasar Uzbekistan da nahiyar turai, wadanda hukumar lafiya ta WHO ta sanar.

“Gwaje-gwajen da ma’aikatar lafiya ta Uzbekistan ta yi, sun nuna cewa, magungunan na dauke da wasu nau’ukan sinadarai na diethlene glycol/ethylene glycos da suka kasance gurbatattu.” Sanarwar ta NAFDAC ta ce.

Hakan ya sa NAFDAC ta nemi al’umar Najeriya da ta gujewa yin amfani da wadannan magunguna.

“Idan kuna da wadannan magunguna, kada a yi amfani da su. Idan kai, ko wani da ka sani ya yi amfani da wadannan magunguna, ko kun fuskanci wata matsala bayan amfani da su, ana ba ka shawara da ka garzaya asibiti don a duba lafiyarka.” NAFDAC ta ce.