Bisa ga alamu nadin da shugaba Jonathan ya yiwa Solomon Arase a matsayin sabon shugaban 'yansandan Najeriya bai yiwa wasu 'yan jam'iyyar APC dadi ba. Tana iya sake zani idan APC ta kafa gwamnatin tarayya.
A farkon wannan makon ne Shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranci majalisar 'yansanda ta kasa, taro na karshe kafin ya bar gwamnati, wadda ta hada da gwamnoni domin amincewa da nadin Solomon Arase a matsayin shugaban 'yansandan Najeriya.
Amma a firar da gwamna Aliyu Wamakko na Sokoto ya yi da wakilin Murya Amurka yace taron da aka yi, wanda ya kasance a wurin, taro ne kawai na bada shawara ba taron tuntuba ba ne na amincewa ko rashin amincewa da Mr. Arase ya zama babban sifeton 'yansanda.
Gwamna Wamakko yace matsayinsu a wurin taron shi ne na bada shawara ba wai amincewa ko rashin amincewa ba. Amma sun dauka cewa a matsayin mai hankali tunda lokacinsa na mulki ya rage kasa da wata daya to ba zai yi wani nadi ba, musamman na shugaban 'yansandan kasa. Saboda gujewa cecekuce ya sa suka yi shiru. Idan an kafa sabuwar gwamnati suka ga cewa Solomon Arase bai cancanta sai su canzashi.
Akan nade-naden da shugaba Jonathan ya yi kwana kwanan nan Gwamna Wamakko yace duk wadannan sun zama wargin yara domin sabuwar gwamnati zata duba ta yi abun da ta ga ya dace. Nade-naden nada wata niyya mara kyau. Misali idan Buhari ya sauke Solomon Arase za'a ce Jonathan ya nada 'dan kudu Buhari ya cireshi saboda ya jawo mashi wahalar siyasa.Yace zalunci ne na 'yan siyasa. Yace duk wani mai hankali ba zai yi abun da Jonathan ya yi yana gaf da mika mulki.
Wamakko yace hankali daban wayo kuma daban. Su Jonathan suna da wayo ba tare da hankali ba.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5