Na’urarorin Zamani Na Son Karin Hurumi a Rayuwa

Baje kolin kayan fasaha da aka yi wannan satin a Las Vegas ya tallata wasu irin kamarorin da ka iya yada yanayin dakin kwana kai tsaye, da wani madubi irin na dakin wanka, amma wanda ke iya nuna siffarka ta yadda za ka san irin kwalliyar da za ta fi inganta kyawonka; da kuma wata irin na’ura mai iya jin numfashin jinjirin da ke ciki.

Wadannan abubuwan na iya zama da amfani – ko akalla su nishadantar – to amma dukkaninsu sun bude kofa ga kamfanoni, da kuma ma’aikatansu su iya leko sirrin rayuwarka.

A wannan satin kawai ma, kafar labarai ta The Intercept ta ba da rahoton cewa wani kamfanin kamarar tsaro mallakar Amazon, ya bai wa ma’aikata damar ganin wasu bidiyon masu huldar cinakayya da shi.

Da bukatar a yi nazari kan ko shin amfanin irin wadannan na’urorin ya kai yadda za a sallama masu sirrin rayuwa. Da farko dai sai ka gamsu cewa kamfanonin da ke irin wadannan na’urorin na kare bayanan ka, kuma ba su yin wani abu da bayanan fiye da abin da su ka ce su na yi.

Ko da kamfani na niyyar kare bayananka, ana iya samun kuskure: Masu kutsen na’ura na iya satar muhimman bayananka. Ko kuma ma’aurata ko abokan zama na iya cigaba da bude wurin ajiyar hotunan bidiyo bayan rabuwa.

“Ba wai tun asali irin wadannan kayan fasahan ba su da kyau ba ne,“ a cewar Franziska Roesner, wani Furfesa a Jami’ar Washington wanda ke nazari kan kariyar kamfuta da kuma sirrin rayuwa.

To amma ta ce har yanzu bangaren kera irin wadannan na’urorin na kokarin daidaita yadda na’urorin za su rika ayyuka masu amfani, a lokaci guda kuma su kare sirrin rayuwar mutane.