Karni na 21, na dauke da abubuwan ban-mamaki da sha’awa, idan akayi la’akari da yadda duniya ke kara dungulewa waje daya, za a ga cewar abubuwa na kara zama cikin sauki ba kamar yadda aka sansu a baya ba.
A wannan zamanin ana iya amfani da kafofin zamani wajen daukar darasi baya ga azuzuwan yanar gizo da ake kira ‘online classes’ sabuwar hanyar daukan darasi itace ta “Virtual Reality” a turance, wadda ake iya saka wani gilashi mutum zai dinga ganin yadda ake gabatar da darasi kamar yana cikin ajin, babu wani banbanci da yadda ake gabatar da darasin a gaban mutum.
Masana sun kirkiri hanyar don saukaka ma mutane da suke wani aiki, ko suke da abubuwa da suke da yawa, don haka mutum zai iya zama a dakin shi da zummar daukan darasi da ake gudanar da shi a wata duniyar.
Ana kuma iya amfani da sautin wasu labarai da suka gabata a baya don hada shiri na musamman da zai bayyana wa mututane yadda abun ya faru a wannacan lokacin, zai zama kamar tarihi.
Amma abun da masanan suka maida hankalin su akai shine, yadda za’a iya samar da shirin cikin rahusa da kowa zai iya saye batare da wata matsala ba.