Wani likita mai suna Lionel Nana a birnin Doula, ya ce a da, idan ya rubutawa mara lafiya magani, maganin ba ya aiki sosai. Amma tun da suka sami wannan na’urar, yana mai tabbatar da cewa sun iya samun ci gaba akalla, kashi 90 cikin 100 ta fannin kula da marasa lafiya.
Ita dai wannan na'ura mai suna True Spec, mai amfani da ita zai dora maganin ne akan ta. Cikin dan kankanin lokaci, na’urar zata yi nazarin sinadiran dake cikin maganin ta kuma tura wa wayar hannun da aka makala mata.
Idan maganin na da kyau, na’urar zata bayyana sinadiran dake kunshe a cikin maganin. Idan kuma maganin mara kyau ne, na’urar zata bayyana cewa bata san sinadiran dake cikin maganin ba.
Na’urar ta sami karbuwa sosai a kwalejin kwararru a fannin magungunan kasar Kamaru, musamman bayan da hukumar lafiya ta duniya ta WHO ta yi gargadin cewa akwai jabun magungunan hawan jinni dake zagaya kasar Kamaru da kuma jabun magungunan cutar sankarau a Niger.
A yanzu, a Kamaru kadai ake samun na’urar. Wanda ya kirkiro na’urar True Spec Franck Verzefe, ya ce wasu kasashen Afrika na muradin samun na’urar.