Wani rahoto da hukumar gwamnatin Amurka ta fitar, na nuni da cewar na’urar daukar bayanan mutane wacce ke amfani da fuska ko ‘yan-yatsu tana nuna wariyar launin fata, jinsi da kuma shekaru.
Na’urar dai tana kin amincewa da duk wani mutum da launin fatar shi ko ita ba fara ba ce, haka idan aka nemi tantance mata sai na’urar ta ki tantance su, kana da tsofaffi.
Amma wannan rahoton da aka fitar a ranar Alhamis, babu tabbacin zai ja hankalin masu rajin kare hakkin bil’adama, wanda yanzu haka hukumomin ‘yan sanda da tashoshin jiragen sama ke amfani da manhajar, wajen tantance mutane da samun cikakkun bayanai akansu.
Tsangayar binciken na’urar kwamfuta ta kwashe shekaru fiye da 20 tana gudanar da bincike, akan na’ura mai tantance mutane, amma ba ta taba maida hankali akan yadda na’urar za ta rika nuna wariya ga wasu mutanen ba.
Babban abin damuwa a nan shi ne, yadda ake ganin na’urar za ta iya haifar da matsalar nuna wariya ga wasu mutane, don haka wannan na'urar za ta bukaci a kara ingantata ta kafin a maida duk wani sakamako da ta fitar na gaskiya.