Na'urar Sanyaya Daki Ta Haddasa Gobara a Ofishin Akawun gwamnatin Najeriya

Yau Laraba 8 ga watan Afirilu gobara ta kona wasu sassan ofishin babban Akawun gwamnatin tarayyar Najeriya dake birnin Abuja, amma bayan sa’a daya an sami nasarar shawo kan gobarar.

A wata hira da Muryar Amurka ta yi da babban Akawun gwamnatin Najeriya Ahmed Idriss, ya ce na’urar sanyaya daki ce ta haddasa gobarar amma an sami nasarar kashe ta ba tare da ta yi wata babbar barna a muhimman wurare ko na’urori na tattara bayanan sirri akan kudaden gwamnatin tarayyar Najeriya ba.

Idriss ya kuma ce ayyukansu basu tsaya ba kuma an yi gyare-gyaren da suka kamata.

Tuni dai wasu suka fara zargin ko da gangan aka tada gobarar da nufin yin rufa-rufa ko boye wani sirri na kashe kudaden gwamnati, musamman a lokacin da masu hali ke bada kudaden tallafi ga gwamnati don yaki da cutar COVID-19.

Da yake maida martini game da zargin, Idriss ya ce jama’a na da damar fadin albarkacin bakinsu, amma kudin gwamnati ba a ofishinsu suke ba, suna ajiye ne a babban bankin Najeriya na CBN. Kaddara ce kawai ta faru, a cewarsa.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Na'urar Sanyaya Daki Ta Haddasa Gobara a Ofishin Akawun gwamnatin Najeriya