Sabuwar na’urar Boris mai wuta da ake kira “Electric Scooter” ta zama ruwan dare a cikin manyan biranen Amurka, wadanda ake amfani da su wajen saukaka tafiya mai matsakaicin zango.
Wani bincike da aka fitar a ranar Laraba, ya yi nuni da cewar akalla mutum 40,000 suka samu ranuka daban-daban.
Daga shekarar 2014 zuwa ta 2018, an samu karuwar adadin mutane da ke amfani da na’urar don saukaka tafiya.
A cewar Dr. Benjamin Breyer, na’urar boris na taikamawa wajen saukaka tafiyar jama’a, don gujewa shiga cikin cunkoson ababan hawa, mutum zai iya amfani da ita ya isa duk inda yake bukata cikin sauri da sauki.
Ya kara da cewar suna fatar su kara wayar da kan jama’a kan hanyoyin amfani da na’urar, tare da daukar matakan kariya, wanda ta haka za’a iya gujewa yawan raunuka da ake samu akan nau’rar ta boris.