Na Sha Wahala Lokacin Jinyar Coronavirus – Gwamna El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i

Kimanin mako guda da sanar da warkewar Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, ya ce ba karamar wahala ya sha ba lokachin da ya yi jinyar cutar coronavirus.

El-Rufa’i wanda ke jawabi game da hadarin cutar coronavirus, ya ce ya kwashe kimanin kwanaki 26 a daki guda ba tare da ya ga fuskar wani ba, ciki har da iyalansa.

Gwamnan ya ce makon farko da aka killaceshi ya sha wahala sosai, saboda tsananin ciwon kai da zazzabi wanda da kyar yake barinsa ya yi sallah, amma ya yi sa’ar rashin samun matsalar numfashi da tari.

Yanzu haka dai an sami almajirai 21 masu dauke da cutar coronavirus a jihar Kaduna, kwamishinar Lafiya ta Kaduna, Dakta Amina Mohd Baloni, ta ce wani mutuum da ya fito daga jihar Lagos shine ya fi tayar musu da hankali, kasancewar basu san inda mutumin ya samu cutar ba.

Gwamnatin Kaduna dai ta ware ranakun Talata da Asabar don sassauta dokar zama a gida, amma Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya yi gargadin duk wanda aka kama ya sabawa dokar gwamnati za ta dauki mataki, domin kare sauran al’ummar jihar.

Domin karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara, daga Kaduna.

Your browser doesn’t support HTML5

Na Sha Wahala Lokacin Jinyar Coronavirus – Gwamna El-Rufa’i - 3'46"