Na San Yadda Zama a Gida Ke Kawo Wa Mara Sa Karfi Kalubale - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Bayan karewar wa’adin hana fita na mako biyu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ayyana a Abuja, Legas da kuma Ogun, ya sake tsawaita wa’adin da mako biyu.

A jawabin da ya yi ga al’ummar kasar, shugaban ya ce kara wa’adin ya zama wajibi don annobar Coronavirus lamari ne na rayuwa da mutuwa.

Kazalika shugaban ya ce ya na sane da yadda lamarin zai kawo kalubale ga talakawa wadanda sai sun fita ne su kan samun abinci, amma duk da haka ba zai yiwuw a sassauta dokar ba.

Hakanan shugaban ya kara da cewa shirin tallafin rage kunci zai cigaba da wanzuwa don taimaka wa jama’a lokacin da su ke zaune a gida.

Shugaba Buhari ya ce wannan lamari ya shafi dukkan kasashen duniya, don Saudiyya ma ta rufe wajajen ibada kamar kuma yadda fadar Vatican ta takaita bukin Easter inda bai fi mutum 10 su ka fito don ranar ba.

A yanzu dai mutum 343 ne ke dauke da cutar ta Coronavirus a Najeriya.