Akpabio ya shigar da kara bayan faduwa zaben dawowa majalisar dattawa inda kafin samun hukuncin babbar kotu, shugaba Buhari ya nada shi a matsayin babban minista mai kula da ma’aikatar yankin Naija Delta.
Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin komawa a sake zaben na Akapabio na jam’iyyar APC da wanda ya lashe zaben a PDP Sanata Christopher Ekpenyong a wasu mazabu.
Akpabio wanda ya fice daga PDP a lokacin ya na shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, ya rubutawa shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomohle cewa ba zai iya barin nauyin da shugaba Buhari ya dora ma sa ya tafi maimaita zaben majalisa ba.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Zubairu Namama ya ce matakin bai sabawa dokar zabe ba, don haka APC sai ta sake zaben fidda gwani don samar da sabon dan takara.
APC ta bakin sakataren walwala Ibrahim Masari ta ce za ta ja hankalin Akpabio ya shigar takarar don ba wata dabara da ta wuce hakan.
A gefe guda shugabar kwamitin zabe ta majalisar wakilai Aishatu Jibir Dukku ta jagoranci tawagar duba zaben majalisa na Burtaniya inda ta ce wani darasi da ya dace 'yan siyasa su koya a Afirka shine kaucewa zaben ko a mutu ko a yi rai.
G karin bayani daga Nasiru El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5