Na Fi Maida Hankali Wajen Wake Jihata - Aminu Genius

A Fannin Nishadi yau, Dandalinvoa ya samu zantawa da wani matashi mai suna Aminu Haruna wanda ke wakokin hip-hop amma amfi sanin sa da suna Genius.

A wata hira da Baraka Bashir, Genius ya fadi cewa a yanzu yafi mai da hankali ne wajen wake asalin sa wato Jihar Jigawa domin duniya ta santa da irin Albarkatun da take dasu.

Ku Duba Wannan Ma Ina Waka Ne Domin Fadakar Da Matasa Illar Kwaya: Aisha Arewa

Genius, mawakin hip hop da Afro pop wanda yace sha’awa ce, ta jashi ga harkar waka tun yana makarantar sakandare a irin kungiyoyin nan da ake kafawa na nishadi, daga nan ne ya fara waka.

Ya kara da cewa cikin irin sakonin da yake isarwa a waka mafi yawa dai sakonnin sun hada da abinda yake faruwa ga al’umma. Ya kuma ce wani lokacin kuma ana duba abubuwan da ke faruwa kusa da mawaki sannan sai mawakin ya wake wannan al’amari .

Your browser doesn’t support HTML5

Nafi Maida Hankali Wajen Wake Asalina: Aminu Genius