Na Fara Sana'ar Hannu Domin Dogara Da Kai: Zainab Sharif

Turaren wuta

A cikin shirin Dandalinvoa na masu kananan sana’o'i yau mun samu bakuncin malama Zainab Sharif Kofar Ruwa matashiya mai sana’ar sayar da turaren wuta da humrah tun kimanin shekaru biyar da suka wuce domin dagaro da kai.

Ta ce ta fara sana’ar hannu ne saboda ita ce sana'ar da ta gani ana yi a gidansu, a kan haka ne ta zamo mai sana’ar dogaro da kai duk da zummar kashe wa kanta kananan bukatu na yau da kullum.

Daga cikin kalubalen da ke ci mata tuwo a kwarya ta ce ya hada da yawan karbar bashi daga abokan sana’ar ta , inda a mafi yawan lokuta, da zarar an karbi turarenta sai su zama surukai da mai saya.

Zainab, ta ce ta na yiwa amare turaren wuta da humrah , sannan ta ce tana kai hajarta kasuwar Kurmi domin ta bayar sari, baya ga masu saya na 'dai 'dai na amfanin su.

Your browser doesn’t support HTML5

Na Fara San'ar Hannu Ne Domin Dogara Da Kai: Zainab