NA AMINCE TSOHON MATAIMAKIN SHUGABAN KASA SHINE UBANGIDA NA

  • Ladan Ayawa

Atiku Abubakar (File Photo)

Gwamnan yayi wannan kalamin ne sailin da yake karban bakuncin wata tawagar shugabannin al’ummar Jimeta ce da suka kai masa ziyara.

A wajen wannan ganawar ce Gwamna Bindow ya bayyana alakar sa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a wannan lokacin ne ya musunta cewa yana da ubangida a yanzu.

Gwamnan dai yana Karin haske akan cewa akwai wasu manya yan siyasan jihar Adamawa da suka tare Abuja amma kullun suna sukan lamirin gwamnatin su domi yaki biya musu bukatun su.

Ga abinda gwamnan ke cewa

‘’Laifi na guda biyu zuwa ukku, na farko ance dome mukeaiki, na biyu bamu bada kudi, to ko kana son ka bada kudin ma ina kudin suke? Kai kaje ka zauna Abuja kace na kawo maka kudi to b azan kai ba kudi na mutanen Adamawa ne kuma dasu zamu yiwa mutanen Adamawa aiki, laifi na ukku shine Gwamna yana tare da Turaki, Don me b azan zauna tare daTuraki domin ko shine ya taimake ni.Ni bana fada da kowa duk wanda ya haife a Adamawa Uba nane, Turaki Ubana ne Nyako Ubana ne ga iyaye na na zahiri suna zaune anan, Duk Jimetan nan bani da Uba da ya wuce Alhaji Idris.Mu yara ne bamu san rashin mutunci b aba a koya muna ba.mu munzo muyi wa mutane aiki ne’’

Kalaman gwamnan dai na zuwa ne lokacin da wasu mutane da kun giyoyi ke mayar da martini game da kalaman sakataren gwamnatin jihar Dr Bindiri yayi na cewa Fulani sune matsalar siyasar jihar Adamawa.

Ga dai Ibrahim Abdul Azeez da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

NA AMINCE TSOHON MATAIMAKIN SHUGABAN KASA SHINE UBANGIDA NA 2'39