A yau Talata aka saki wasu ‘yan jarida biyu na kamfanin dillancin labarai na Reuters, da aka kama a kasar Myanmar, bisa zargin karya dokar sirrinta bayanai, da aka kafa tun kafin kasar ta sami ‘yancin kanta daga ‘yan mulkin mallaka.
Wa-Lone da Kyaw Soe Oo na daga cikin dubban fursunoni da shugaban kasar Wyn Myint ya yi ma afuwa, a karkashin shirin afuwa na kowace shekara, da hukumomin kan tsara don murnar shagulgullan tarbon sabuwar shekarar gargajiya, wanda kuma aka faro tun daga ranar 17 ga watan Afrilu.
Dandazon ‘yan jarida sun tarbe su, lokacin da suka fito bakin kofar gidan yarin mafi tsanani da ke birnin Yangon.
Wa Lone, ya ce a shirye yake ya ci gaba da aikin shi na jarida, ya kuma kara da cewar, “ai har na kosa na koma dakinmu na watsa labarai.”
A watan Satumba ne dai aka yanke wa ‘yan jaridun biyu hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari, biyo bayan daukar labarai da suka yi na irin gallazawar da sojojin kasar suka rinka yi wa mutanen jihar Rakhine da ke arewa maso yammacin kasar ta Myanmar.
Lamarin ya tailstawa dubban 'yan kabilar Rohingya suka yi gudun hijira zuwa kasar Bangladesh a shekarar 2017.