Mutum mutumin dan wasan kwallon kafa na Liverpool, dan Kasar Masar Mohamed Salah wanda aka kaddamar a kasarsa ta haihuwa ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
An kaddamar da mutum mutumin ne a wajan wani taron biki na Matasan Duniya da aka gudanar a Sharm Al-Sheikh ranar Lahadin da ta gabata.
Mutum mutumin ya nuna hannayen dan wasan a bude kamar yadda yake yi idan ya zura kwallo a raga.
Mutane da dama sun ce mutum mutumin bai yi kama da Salah ba, yayi kama ne da mawaki Leo Sayer, ko kuma Marv na cikin fim din Home Alone.
Mutum mutumin na Salah ya bi jerin na 'yan wasan kwallon kafa da aka yi su a kasashe daban-daban, wanda hakan ya sanya magoya bayansu cewar sam sam basu yi kama da su ba.
Ku Duba Wannan Ma Sau Nawa Barcelona Da Real Madrid Suka Kara?An kwatanta mutun mutumin Salah da na Cristiano Ronaldo wanda aka rika zolaya bayan an kaddamar da shi a filin jirgin saman Madeira a shekarar da ta wuce.
Wanda ya sasaka mutum mutumin Emanuel Jorge da Silva Santos, ya bayyana bacin ransa kan sukar da aka rika yi masa a shafukan yanar gizo bayan da ya yi aikinsa.
Taron matasan, ya samu halartar dubban mutane, ciki har da shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi. Kuma wannan taron shi ne karo na biyu, domin wanzar da zaman lafiya a kasar Masar.
Your browser doesn’t support HTML5