Yadda ake amfani da na’urar mutun-mutumi a kamfanoni da ma’aikatu a Amurka, ya nunka sau ukku akan yadda ake amfani da shi tun daga shekarar 2009 zuwa 2017. An kuma samun karancin aiki a manyan kamfanoni, tattalin arziki kuwa ya karu ba kamar shekaru 10 da suka shige ba.
An samu karuwar tattalin arziki wajen amfani da kimiyya da fasaha, da mutunmutumi, wanda ya taimaka matuka wajen kara samuwar kudaden shiga, amma kuma mutane sun rasa ayyukansu. Farfesa William M. Rodgers, na jami’ar Rutgers, wanda ya wallafa wani rahoto da ke nuna cewar, mutane da dama sun rasa aikin yi.
Baya ga rashin aikin yi ga wasu mutane, da dama kuma sun samu raguwa a albashin su, sabo da ire-iren ayyuka da suke yi ana iya ba mutunmutumi yayi, ba tare da an biya shi wasu kudi ba, hakan yasa kamfanoni rage albashin ma’aikata.
Binciken ya kara da cewar, akwai wasu jihohin Amurka da mutunmutumi ke rike da akasarin aikin da ake yi a wasu fannoni rayuwar yau da kullun, jijojin Michigan, Ohio, Illinois da Wisconsin suke kangaba wajen mika ragamar aiki ga mutunmutumi, musamman a kamfanoni da ake kere-kere.
Mutunmutumi kanyi aikin shirya kaya, rufewa da bude abubuwa, walda, faynti da dai makamantansu cikin tsafta. Sauran jihohin da ke biye wajen danka aikin mutane ga mutunmutumi kuwa, sun hada da Los Angeles-Long Beach-Santa Ana, California, Chicago-Naperville-Joliet, Illinois, Houston-Baytown-Sugar Land, Texas.
Sai Phoenix-Mesa-Scottsdale, Arizona, Detroit-Warren-Dearborn, Michigan, Milwaukee-Waukesha-West Allis, Wisconsin, Philadelphia-Camden-Wilmington, Pennsylvania/New Jersey/Delaware/Maryland, San Jose-Sunnyvale-Santa Clara, California, Indianapolis, Indiana, da Cleveland-Elyria, Ohio.