Mutum Na Biyu Da Ya Kamu Da Cutar Ebola a Congo Ya Mutu

Fiye da mutane 2,500 suka kamu da cutar Ebola tun bayan barkewar cutar a watan Agusta 2018.

Jami’ai a Jamhuriyar dimokaradiyar Congo, sun ce mutumin nan da aka tabbatar da shi ne na biyu da ya kamu da cutar Ebola a garin Goma ya mutu.

A yau Laraba, aka fitar da wannan sanarwa, kwana guda bayan da aka gano mutum na farko da ya kamu da cutar.

Mutum na farko da ya kamu cutar, ya yi tafiya zuwa garin Goma daga wani yanki na karkara da ke arewa maso gabashin Lardin da ake kira Ituri.

Kwanaki kadan bayan isowarsa, aka gano yana dauke da cutar, an kuma sa shi karkashin kulawa a Cibiyar Kula da masu fama da cutar ta Ebola a Goma.

Shi dai Goma, gari ne mai yawan mutane sama da miliyan daya, yana kuma karshen kasar ta Congo ne, wacce ta hada iyaka da kasar Rwanda, wacce a kullum, dubun dubatar mutane ke ketarawa cikinta a kafa.