Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce matsalar yunwa na ci gaba da karuwa a yankin Yammacin nahiyar Afirka.
Washington D.C. —
A cewar jami’an, mutum miliyan 48 ne suke fuskantar barazanar yunwa, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikice.
Jami’an sun bayyana hakan ne a Dakar, babban birnin Senegal a ranar Talata yayin wani taro da suka yi, inda suka ce matsalar ta samo asali ne daga rikice-rikice da annobar COVID-19 da kuma matsalar hauhawar farashin kayayyaki.
A cewarsu, kasashen da lamarin ya shafa sun hada da Burkina Faso, Mali, Niger, Arewacin Najeriya da kuma Mauritania.
Akalla mutum dubu 45 ne suke gab da fadawa kangin matsalar matsananciyar yunwa a yankin Sahel kamar yadda jami’an suka bayyana, adadin da ya zamanto sabon abu a yankin.