Rundunar ‘yan sandan kasar Kenya sun bada rahoton cewa mutum guda ya rasa ransa, kuma ma’aikata hudu ‘yan kasar waje sun bace bayan wani harin da ‘yan ta’adda suka kaiwa sansanin ‘yan gudun hijira na Dadaab kusa da kan iyaka da Somalia, da hantsin yau Juma’a.
Kwamishinan ‘yan sandan lardin Dadaab Albert Kimathi, ya shaidawa muryar Amurjka cewa an kai harin ne hususan domin jikkata ayyukan rarraba kayan agaji, domin cibiyar rarraba kayan agaji karkashin kulawar Norway ce aka dosa da harin.
Kwamishinan yace jami’in da ya fara rasa ransa dan kasar Kenya ne, sai kuma jami’an kasar waje hudu da aka sace. Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa: duka-duka jami’an kasar waje hudu ne, daya dan kasar Norway, daya kuma dan kasar Colombiya, dayan kuma dan kasar Pakistan ne sai kuma dan kasar Phillipine guda. Duka-duka jami’ai hudu ke nan ‘yan kasar waje.
Sai dai kuma kwamishinan ‘yan sanda Kimathi yaki bayani kan ko ‘yan sanda sun kai wani farmaki maida martini da kuma shirin neman inda ake boye da turawan. Gefe daya kuma sakatare janar ta hukumar kula da ayyukan agaji ta Norway, Elisabeth Rasmusson wadda ke tare da ma’aikatan agajin cewa tayi an kai harin ne kuryar sansanin da ake dauka nada cikakken tsaro sannan taci gaba da cewa:
tana kyautata cewar ‘yan bindiga hudu ne suka kaiwan jami’an hari, kamar yadda ta gani da idonta.’Yana bindigar suka rika harbi hagu da dama, sannan suka je suka sace mota guda. Ba’a Ankara ba sai bayan sun tsere sai muka ga babu jami’ai hudu daga cikin ma’aikatan cibiyar ayyukan agajin. Hukumomin kasar Kenya dai sun aza laifin kai hare-haren sansanin ‘yan gudun hijira a kan mayakan al-shabab. Amma kuma al-shabab ta musanta cewar tana da hannu a satar jami’ain ayyukan agaji a sansanin ‘yan gudun hijirar dake Kenya.