Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewa yanzu mutum 65 ne ke dauke da cutar Coronavirus a kasar.
A sanarwar da hukumar ke fitarwa ta ce, mutum 44 ne aka sama da Cutar a binin Legas, 11 a Abuja, 3 a Ogun, 1 a Ekiti, 1 a Oyo, 1 Edo da 2 a Bauchi, 1 a Osun da kuma 1 a Rivers.
Har ila yau hukumar ta ce an salami mutum 3, bayan sun warke daga cutar yayin da 1 ya rasu.
A jawabin ministan yada labarai na kasar Lai Mohammed ya ce gwamnati na duba yiwuwar rufe zirga zirga tsakanin jihohin najeriya 36 domin rigakafin bazuwar cutar.
Suma kanfanonin jiragen saman najeriya masu zaman kansu sun ce daga yau ne akasarin su za su dakatar da zirga zirga a kasar domin kare ma’aikatansu da kuma yan Najeriya daga kamuwa da wannan cutar ta Coronavirus.
A cewar hukumar lafiya ta duniya mutum fiye da 500,000 ne suka kamu da cutar, a yayin da kuma fiye da 22,000 suka rasa rayukansu.