Hukumar kare hadurra a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, FRSC, ta tabbatar da mutuwar mutum 28 sanadiyyar wani mummunan hadarin mota da ya faru.
Bayanai sun yi nuni da cewa, wasu motoci biyu ne suka yi taho-mu-gama akan babbar hanyar Bauchi zuwa Kano, a kusa da wani gari mai suna Gubi.
Dukkan fasinjojin da ke cikin motocin biyu sun kone kurmus, ta yadda ba a iya gane kowa, a cewar hukumomi.
A hirarsa da wakilin Muryar Amurka a Bauchi, Kwamandan shiyyar hukumar kare hadurra, Abdulrazak Najume, ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa barci ne ya kwashe daya daga cikin direbobin biyu.
Najume ya ce, direban babbar motar, ya fado waje bayan da kofarsa ta bude, dalilin da ya sa kenan bai mutu ba.
Ya kuma jaddada muhimmancin kiyaye dokokin tuki, yana mai cewa, dole mutane su daina cunkusuwa a cikin motoci.
A saurari rahoto cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5