Mutum 248 Sun Sake Kamuwa Da Coronavirus a Najeriya

A cikin sabbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka a Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar.

A cewar NCDC, mutum 248 ne cutar ta sake harba, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 4,399 a kasar.

A cikin wadannan sabbin mutanen da suka kamu da cutar akwai ‘yan Legas 81, ‘yan Jigawa 35, ‘yan Borno 26, da kuma ‘yan Kano 26.

Wadannan jihohin su ne jihohi 4 cikin wadannan alkaluman da cutar ta fi kama mutane, baya ga sauran jihohi da kuma birane.

Tun da aka sassauta dokar takaita zirga-zirga a Najeriya adadin wadanda ke kamuwa a kullum ya karu daga kasa da 100, zuwa kusan dari 300 a kullum.

Wasu rahotanni na nuni da yadda mutane ke yawo a jihohi da kuma biranen da aka sassauta dokokin takaita zirga-zirga ba tare da sanya takunkumin hanci ba da kuma ba da tazara kamar yadda hukumomin kiwon lafiya suka ba da shawarar a yi.

Shi ma gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu inda cutar ta fi kamari a kasar ya fitar da wata sanarwa inda ya shawarci ‘yan Legas din da su kara mayar da hankali wajen bin sharuddan da aka ce a bi.

Ya zuwa yanzu mutum 143 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar, yayin da mutum 778 suka warke kuma.