Mutum 213 Suka Kamu Da Cutar Lassa Fever - Hukumomin Najeriya

Wani jami'in kula da lafiya yana duba wani mai fama da cutar Lassa Fever

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce, tana kara himmatuwa wajen ganin ta shawo kan cutar zazzabin Lassa, wacce ke ci gaba da yaduwa cikin gaggawa a sassan yammacin Afirka.

Yankin yammacin na Afirka na tsakiyar lokacin da cutar ta fi kamari, wacce ta fi tasiri a tsakanin watan Disamba da Maris.

Hukumar ta WHO ta ce, da ma dai ana sa ran barkewar cutar a dan tsakankanin wannan lokaci, amma a cewar Kakakin hukumar ta WHO, Tarek Jasarevic, sun damu matuka kan yadda cutar ke yaduwa cikin gaggawa.

A cewar Kakakin, akwai bukatar al’umomin yankin na Yammacin Afirka, su dauki matakan tsabtace muhallansu domin kare kansu daga kamuwa da wannan cuta.

"Misali, ana so mutane su rika ajiye kayayyakin abincinsu a wuraren da beraye ba za su iya kai wa ga ba, da zubar da shara nesa da gidajensu.” Inji Tarek Jasarevic.

A ranar 22 ga watan Janairu, Najeriya ta ayyana barkewar cutar, inda ta ce jihohi 16 ne ke fama da ita.

Hukumar dakile yaduwar cututtukan, ta tabbatar da cewa mutum 213 ne suka kamu da cutar a duk fadin kasar, yayin da wasu 42 suka mutu.

Wannan kuma shi ne lokaci da cutar ta fi girma a cewar hukumomin Najeriya.