Mutum 210 Cutar COVID-19 Ta Harba a Najeriya

Wasu ma'aikatan lafiya da ke kula da masu fama da cutar coronavirus

Mutum 210 suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya a cewar hukumar da ke kare yaduwar cututtuka ta NCDC a kasar.

Adadin ya kai haka ne, bayan da aka samu karin mutum 26 da cutar ta harba a kasar kamar yadda NCDC ta sabunta alkalumanta a shafinta na yanar gizo a ranar Juma’a.

“Daga cikin mutum 26; 11 a jihar Legas suke, takwas a Osun, uku a Abuja, uku a Edo sannan daya a Ondo.”

Amma duka sabbin mutanen da suka kamu da cutar, ba su nuna wata zazzafar alamar cutar ba, a cewar NCDC.

Hukumar ta kuma ce ya zuwa yanzu, mutum hudu ne suka mutu sanadiyyar cutar sannan an sallami wasu 25 bayan da suka samu sauki.