Sai dai ‘yansanda basu bayyana dalilin wannan lamari ba amma dai sunce basu tsammani yana da nasaba da aikin ta'addanci, sai dai kila wani abu ne tsakanin wasu mutane wanda suke da alaka da harkan kasuwanci.
Jamiian ‘yansanda suka ce suna nan suna bincike domin gano wadanda ake tuhuma, suka ce sunfi danganta shi da gaba wanda keda alaka da kasuwanci, kuma mutum daya ne ko kuma fiye aka yi niyyar kaiwa harin, inji mukaddashin sufetan ‘yan sandar jihar Selangor Abdul Rahim Jafar.
Abdulrahim ya tabbatar cewa abinda ya fashe gurneti ne.
Wani ma'aikacin gidan sayar da abubuwan shaye-shaye dake Movidar a garin Puchong dake wajen babban birnin kasar Kuala lumpar yace a kalla manyan mutane masu kudi ko kuma ‘yan kasuwa ne suke kallon wasan da aka buga tsakanin Italy da Spain lokacin da wannan gurneti ya tashi