Cikin shekarar da ta gabata, rikici ya daidaita yankin Kasai na Congo inda mutane miliyan 1.4 suka fice daga gidajensu, rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 3 tare da barnata bakin dayan kauyukan yankin, a cewar Claude Jibidar, jami’in da ke kula da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo.
Ya kara da cewa yanayin da ake ciki a yankin za a iya kwatanta shi da abinda ke faruwa a Syria da Yamal.
Yanzu haka Congo wacce makekiyar kasa ce dake tsakiyar Afirka, tafi kowa ce kasa yawan mutanen da rikici ya tilastawa ficewa daga gidajensu a nahiyar Afirka.
Ba hukumar samar da abincin ce kadai take janyo hankula kan halin da ake ciki a kasar ta Congo ba, kungiyar likitoci ta kasa da kasa, wato Doctors Without Borderss a kwanan nan ta yi gargadi kan matsalar yunwa a tsakanin yara kanana, inda akan samu matsananciyar yunwa da ta kai kashi goma a wasu yankunan.