A cikin daren jiya ne kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijer, Alhadji Zakariya, ya bayyana a kafofin yada labaran kasar domin sanar da ‘yan kasar a hukumance irin yanda ‘yan ta'adda su ka abka wa wadansu garuruwa da wata tunga a jihar Tahoua a cikin gundumar Tilliya har suka kashe mutane 137.
‘Yan ta'adda ne suka abka wa wadanan garuruwan na gundumar Tilliya su ka hallaka fararen hulla da ba su ji ba ba su gani ba.
Su dai wadannan 'yan ta'addar sun kai kololuwa wajen aikata danyen aiki, tun da ba su abka wa kowa sai fararen hulla, inji kakakin Gwamnatin kasar.
Ya ci gaba da cewa, gwamnati ta soma bincike domin gano wadanda su ka aikata wannan mumunan aikin, domin daukar matakin doka, ciki har da gurfanar da su gaban kuliya.
A cikin wannan mummunan yanayin, gwamnati ta kebe kwanaki uku na zaman makoki, kuma za a sauko da tutocin tsakiya, haka ma shugaban kasar da gwamnati na isar da sakon ta'aziyarsu ga wadanda suka yi rashi, tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikata.
Haka ma, ta yi Allah wadai da danyen aikin wadannan ‘yan ta'adda, kuma ta na kira ga ‘yan kasar da su kiyaye da duk abin da ke kai komo, domin hukumomin Nijer sun lashi takobin ci gaba da yakar ‘yan ta'adda har sai sun cimma nasara.
Ga dai cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5