Mutanen Da Suka Mutu a Guguwar Idai Sun Haura 300

Jami'ai sun tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu a muguwar guguwa mai suna Idai wanda afkawa yankin na kudancin nahiyar Afrika Mozambique, Zimbabwe da Malawi sun zarta 300.

Yau kwana biyu da kasar Mozambique ta ayyana zaman makoki da juyayi bayan da wata muguwar guguwa mai suna Idai ta afkawa yankin na kudancin nahiyar Afrika, har daruruwan mutane suka mutu..

Jami'ai sun tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu a Mozambique, da Zimbabwe da kuma Malawi ya zarta 300.

Kwararru a fannin yanayi, sun yi hasashen cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yau Alhamis kuma yawan ruwan da yayi ambaliya na dada karuwa. Ƙungiyoyin kai agaji na can na ƙoƙarin kai kayayyakin agaji ga wadanda suka tsira kuma suke matukar bukatar kayan.