Ibrahim Magu Yayi Bayani Kan Sasantawa Da Wadanda EFCC Ke Tuhuma

Yayin da ake ci gaba da tuhumar manyan jami'an gwamnati da na soji da wawure kudaden gwamnati da yawa daga cikinsu sun bukaci da ayi sulhu, don su maida.

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bada tabbacin samun bukatu daga mutanen da ake tuhuma da yin sama da fadin dukiyar gwamnati wasunsu har an gurfanar da su. Sun nemi da ayi sulhu domin su dawo da kudaden da suka sace.

Sai dai yace, tilas ne hukumarsa ta bi ka'ida da yin nazari domin a bi hanyoyin da jama'ar kasar zasu fi sha'awar gani anyi na ladabtar da jama'ar da ke neman wannan alfarmar ta yadda na baya za su yi koyi gobe ba za su yi ba.

Daga cikin wadanda aka samu bukatunsu sun hada da tsohon sakataren yada labarai na Jam'iyyar PDP Olisah Metuh wanda aka tuhuma da satar Naira miliyan 400 da tsohon shugaban sojojin saman Najeriya Muhammad Dikko Umar.

Domin karin bayani, saurari rohoton Umar Farouk Musa

Your browser doesn’t support HTML5

Mutanen da EFCC ke tuhuma suna neman ayi sulhu - 4' 02"