Mutane takwas sun mutu a wadansu fashe fashe yayin bukin 'Yancin Kan Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan yana gaida jama'a yayin bukin tunawa da cika shekaru 50 da samun 'yancin kai, a Abuja, Nigeria, ranar Jumma'a, 1 ga watan Oktoba, 2010.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace a kalla mutane takwas ne suka mutu a wadansu tagwayen fashe fashen bom da suka auku dab da inda ake gudanar da bukuwan samun ‘yancin kai.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya tace a kalla mutane takwas ne suka mutu a tagwayen fashe fashen bom da aka kai dab da inda ake gudanar da bukuwan samun ‘yancin kai. Fashe fashen sun auku ne ranar jumma’a daya bayan daya a harabar ma’aikatar shari’a dake kimanin tazarar tafiyar minti goma da inda aka gudanar da bukuwan samun ‘yancin kan. Bisa ga dukan alamu an tada nakiya ta biyu ne da nufin tsinkayar wadanda zasu kai dauki a harin na farko. Akwai sabanin rahotanni kan fashewar nakiya ta uku a filin Eagle Square inda shugaba Goodluck Jonathan da dubun dubatar mutane suke bukukuwan cika shekaru hamsin da samun ‘yancin kai. Fashewar ta biyo bayan barazanar kai harin bom da kungiyar mayakan nan da tayi kaurin suna "Movement for the Emancipation of Niger Delta" tayi. A cikin sakon da ta aika ranar jumma’a, kungiyar tace “yan Najeriya basu da dalilin buki,” bisa ga cewarsu, an shafe shekaru hamsin ana sacewa mutanen yankin Niger Delta mai arzikin man fetir kasarsu da kuma arzikinsu. Shugaba Goodluck Jonathan yace wadanda suka aikata wannan mugun laifin zasu dandana kudarsu.