A makon jiya wurin taron bashi wata lambar yabo a Legas Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya sake cewa bai kamata gwamnatin Najeriya ta cigaba da biyan kudin tallafin mai ba muddin tana bukatar tattalin arzikin Najeriya ya daidaita..
Kazalika sarkin wandan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ko CBN ne ya caccacaki bankin dangane da yadda ya ki karya darajar Nera.
Wadannan kalaman nashi sun haifar masa da martani daga jama'a da kungiyoyi da ma masana tattalin arziki da ma wasu.
Wani Isyaku Lawal yace suna girmamashi a matsayinsa na sarkinsu da kuma masanin tattalin arziki. Shi yace idan an cire tallafin man fetur 'yan kasa zasu ji dadi. Amma a yadda farashin yake yanzu 'yan kasa basu ji dadin ba kuma babu man. Kana babu wani cigaba da aka samu. Yanzu kuma yace a karya darajar Nera wai kasa zata cigaba. Babu yadda za'a yadda dashi.
Shi ma Nura Umar cewa ya yi lokacin da yake gwamnan babban bankin Najeriya cewa ya yi a cire tallafi wai man fetur zai samu ilimi kuma zai wadata kuma rayuwa zata yi sauki. Duk wadannan ukun babu su.Idan an karya Nera kaya zasu yi tsada.
Ita ma kungiyar kwadago ta Najeriya ta kira shugaban kasa Muhammad Buhari da ya yi watsi da kiraye kirayen Sarkin Kano na cire tallafi ko karya darajar Nera.
Wani malamin kwalajin fasaha a Kano yace abun da sarkin ya fada ya sabawa yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5